Kano Book Club tare da haɗin guiwar The Third Space, na farin cikin sanar da Gasar Bashir Tofa. Gasa ce da aka ƙirƙira domin bunƙasa al’adu da adabin Hausa. Manufarmu ita ce mu tallafa wajen haɓaka rubutun Hausa da kuma samar da adabi.
An sanya wa gasar sunan ne don girmama Bashir Othman Tofa (1947–2022)—shahararren ɗan siyasa, marubuci, kuma wanda ya bada gudunmawa ga harshe da al’adun Hausa. Wannan gasar ƙoƙari ne na girmamawa da kuma saka wa fitattun gajerun labarai da aka rubuta da Hausa, domin tabbatar da cewa harshen da al’adunsa suna ci gaba da bunƙasa. al’adunsa suna ci gaba da bunƙasa.
Lokacin Aika Labarai:
📅 Buɗewa: 1 ga Afrilu, 2025
📅 Rufewa: 15 ga Mayu, 2025
Kyautar Da Za a Bai Wa Wanda suka yi Nasara:
- Zakaran Gasa: Naira 150,000
- Na Biyu: Naira 100,000
- Na Uku: Naira 50,000
- Akwai yiwuwar haɗa gajerun labarai goma mafi kyau wuri ɗaya a matsayin littafin ƙagaggun labaran Hausa
Wanda Suka Cancanci Shiga:
- Dukkan marubuta ‘yan shekara 18 zuwa sama
- Dukkan marubutan da ke iya rubuta labarai da Hausa
Ka’idojin Gasa:
- Wajibi ne labari ya kasance ƙagagge
- Wajibi adadin kalmomin labari su kasance tsakanin 2000 – 3000 a kan kowane jigo
- Wajibi ne a rubuta labarin da harshen Hausa
- Za mu karɓi fassarar labarin Turanci da marubuci ya rubuta da kansa kuma bai taɓa wallafawa ba
- Girman haruffa: 12 EB Garamond
- Tazarar layi: ninki biyu
- Wajibi ne aikin ya kasance na asali kuma ba a taɓa wallafa shi ba
Ka’idojin Miƙa Aikin:
- A turo labari a matsayin ‘Word document’ zuwa: thethirdspace2024@gmail.com
- A sanya sunan fayil ɗin kamar haka: BTP_Sunan Labari_Kwanan-wata; misali: BTP_Mutumin Kirki_01-04-2025
- A sanya adadin kalmomi a shafi na farkon daftarin
- Kar ka/ki sanya sunanku a ko’ina a cikin daftarin
- A jigon saƙon imel, a rubuta: BTP Entry/Sunan Labari/Kwanan-wata /Sunanka misali: BTP Entry/Mutumin Kirki/01-04-2025/Usman Balarabe
- A cikin imel ɗin, sanya sunanka/ki, hanyoyin tuntuɓa da taƙaitaccen tarihinka/ki (cikin kalmomi 100)
- Idan labarin fassara ne daga Turanci, a bayyana hakan a cikin imel sannan a saka sunan mai fassara (kai ko wani). A kuma haɗa da ‘Word document’ da ke ɗauke da labarin cikin Turanci
- An yarda da aika labari a wasu wuraren bayan na mu, amma da zarar an sanar da shi a wata gasar ko an sanya shi cikin jerin zakarun gasa, a sanar da mu hakan nan da nan
Za a sanar da sakamakon kuma a ba da kyautar a Kano tsakanin watan Yuli da Agusta 2025.
Wannan dama ce ta musamman don bayar da gudummawa ga tarihin adabin Hausa tare da samun girmamawa da yabo da suka dace. Muna ƙarfafa guiwar dukkan marubuta da masu ba da labarai da ke da sha’awa da kuma kishin Hausa da adabinsa da su miƙa aikinsu.
Domin ƙarin bayanai da tambayoyi, tuntuɓi The Third Space a dukkan shafikan sada zumunta.